An gano mutumin da ya kai hari a Paris

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane da dama sun jikkata a harin da aka kai Bataclan.

Firai Ministan Faransa, Manuel Valls, ya ce 'yan sandan kasar sun gano mutum na uku cikin mutanen da suka kai hari a gidan rawa na Bataclan da ke birnin Paris a watan jiya.

Mutane 90 aka kashe a harin da aka kai a gidan rawan.

Mista Valls bai bayyana sunan mutumin ba, sai dai bai karyata rahotannin da ke cewa sunan mutumin Fouad Mohamed-Aggad daga jihar Strasbourg ba.

Wata jaridar kasar, Le Parisien, wacce ta ambato wasu "majiyoyi masu tushe", ta ce mutumin ya koma Faransa ne daga Syria.

Sauran mutane biyu da suka tayar da bama-baman da ke jikinsu a gidan rawar su ne Omar Ismail Mostefai, dan shekara 29, da Samy Amimour, dan shekara 28, kuma dukkansu 'yan Faransa ne.