Za a dawo da karbar "kudaden hanya"

Image caption Za'a dawo da kofofin karbar kudade a kan manyan hanyoyin Najeriya ne domin samun kudin shiga

Gwamnatin Nigeria ta ce za ta dawo da kofofin da ake karbar kudade na kan manyan hanyoyin kasar.

Ministan makamashi da gidaje da ayyuka, Baba Tunde Fashola ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Ministan ya ce gwamnatin za ta dawo da tsarin ne dan tabbatar da nagarta da kuma gyaran hanyoyin.

Za kuma a yi amfani fasahar zamani wajen karbar kudaden a wurin masu wuce wa ta kofofin.

Gwamnatin tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ce ta sa aka rushe kofofin da aka gina kan manyan hanyoyin kasar bayan da ta soke tsarin a lokacin da ta soma biyan tallafin man fetur.