'An caccaki kalaman Trump kan Musulmi'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kalaman Mr Trump sun janyo babbar suka daga dukkanin bangarorin siyasu na kasar

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta yi gargadi cewa musayar kalaman da ake yi a yakin neman takarar shugabancin Amurka yana yin illa a kan shirin tsugunar da 'yan gudun hijirar Syria a Amurka.

Mai magana da yawun hukumar ta yi wannan bayani ne a matsayin raddi ga kalaman daya daga cikin masu son yin takarar shugabanci a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump wanda ya yi kira da a hana Musulmai shiga kasar kwata-kwata.

Ta ce irin wadanan kalamai da gwamnonin jihohin Amurka da dama suka yi na sanya abin da ta kira muhimmin shirin sake tsugunar da 'yan gudun hijira a tsaka mai wuya.

Kalaman Mt Trump sun janyo babbar suka daga dukkanin bangarorin siyasa na kasar.

Amma shi Mt Trump ya ce yana nan a kan kalamansa.

Sai dai daraktan majalisar da ke hada kan Musulmai Amurkawa, Nihad Awad, ya shaida wa BBC cewar Donald Trump mutum ne da ke da hadari ga zaman lafiya: