Boko Haram: Ina iyayenmu ?

'Yan gudun hijira da ke samun mafaka a wani sansani a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijira da ke samun mafaka a wani sansani a Najeriya

A Najeriya, mutane da dama da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu na kukan cewa ba su san inda sauran 'yan uwansu suke ba, ciki har kananan yara.

Hukumar agajin gaggawa ta kasar, NEMA dai ta ce yanzu haka akwai kananan yara kimanin dubu biyar wadanda har yanzu ba su san inda iyayensu suke ba.

Hukumomin agaji dai sun ce ko da ya ke an samu raguwar adadin irin wadannan mutane, amma har yanzu matsalar na da girman gaske.

Wasu daga cikin irin wadannan yara dai na cikin kuncin rayuwa, amma a wasu lokutan sukan yi wasanni kamar kwallon kafa domin debe wa junansu kewa.

Fatima Salihu wata mata mai shekara arba'in da takwas da haihuwa, ta shaida wa BBC cewa daga cikin 'ya'yanta biyar ba ta ga uku ba, kana shi ma mijinta ba ta jin duriyarsa ba tun bayan da tarzoma ta raba su a garin Michika da ke jihar Adamawa.