Gwamnatin Borno ta tabbatar da sace mata a Bamburatai

Kwamitin da gwamnatin jihar Borno ta Najeriya ta kafa kan zargin sace mata a garin Bamburatai da ke karamar hukumar Bui ya tabbatar da cewa an sace mata shida a harin da aka kai a garin a watan Nuwamban da ya gabata.

Sai dai a cikin rahoton da kwamitin ya gabatarwa gwamna Kashim Shettima, ya ce ba su tabbatar ko mayakan kungiyar Boko Haram ne suka yi awon-gaba da matan ba.

Kwamitin ya kara da cewa jarirai na cikin wadanda aka sace.

Kwamitin ya gano cewar masu tayar da kayar baya sun kai hari da misalin karfe goma na dare a watan daya gabata inda suka rika harbi a kan mai-uwa-da-wabi kuma suka kona gidaje da dama .

A baya dai, wasu kafofin watsa labarai sun ce mayakan kungiyar Boko Haram sun yi awon-gaba da mata da dama a kauyen Bamburatai.