Wasika daga Afrika: A daidaita sahun manyan Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari, ya lashi takobin yaki da karbar hanci da rashawa a Najeriya, kasar da ta fi kowacce girman tattalin arziki a Afrika.

A sharhinmu na wasikun 'yan jarida, marubuciyar nan Adaobi Tricia Nwaubani, ta duba yadda sabbin matakan tsuke bakin aljihu ke shafar tattalin arzikin Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki ne a watan Yunin bana, kuma bisa ga dukkan alamu yana daukan duk wasu matakai da zasu sa manyan mutane su kauracewa aikin gwamnati.

Baya ga albashin da majalisar zartarwa ke samu wanda aka sanya wa idon ba sani ba sabo, saboda halin ha'ula'in da tattalin arzikin kasar ya shiga da ba a taba ganin irinsa ba a shekarun da suka gabata, shugaban ya bayar da umurnin a rage tawagar dukkanin ministoci.

Manyan Najeriya kalilan ne ke tafiya babu tawagar dake biye dasu, yawanci masu mukamin gwamnatin kasar da ta fi kowacce a Afrika yawan mutane na tafiya ne da jama'a da dama da ke rufa masu baya, inda suke masu rakiya zuwa bukukuwa ko zaman makoki da sauransu, shi kuma yana musu alkhairi, ya kuma kula da duk wasu bukatun su.

'Kasar Najeriya'

Kasar da ta fi kowacce a Afrika girman tattalin arziki da kuma yawan al'umma, ga arzikin man fetur, amma duk da haka tana fuskantar karayar arziki sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Kashi 62.6 cikin dari na al'ummar kasar su miliyan 170, suna cikin matsanancin talauci.

Yawan taron jama'ar da za ka lura da shi a wuri, misali ko Otal ko kuma dakin sayar da abinci, zai nuna alamun wani babba zai ziyarci wurin, inda suke mamaye abun hawan sa ko kuma su fada cikin nasu su masa jagora.

Ba sabon abu bane a Najeriya, kasar da ke da kabilu dabam-dabam, inda aka san sarakuna da yawo da marokan da basu da wani aiki sai koda sarakunan.

Hakkin mallakar hoto Adaobi Tricia Nwaubani
Image caption Marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani.

Kwanakin baya da marubuciyar, Adaobi Tricia Nwaubani ta gayyaci abokin ta, Rick wani taro, inda shi da kan sa ya ja hankali ta da cewa, tunda har ta gayyace shi to ta gayyato wata tawagar, yana mai cewa, "Shin kin shirya yin hakan?"

A bara ne ya gaji sarautar gargajiyar garinsu bayan mutuwar mahaifinsa, hakan kuma ya sauya matsayin sa daga dan makarantar da suka taso tare, zuwa wanda idan har ta gayyace shi taro, to dole ne a shiryawa tasa tawagar.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu sarauta suna samun daukaka matuka a Najeriya.

'Tsattsauran ra'ayin shugaba Buhari'

An san jami'an gwamnati maza da mata da daukan mutane da dama a matsayin kananan mataimaka, inda kowanne cikin su ke zukar albashi daga ma'adanin kudin gwamnati.

A lokacin da shugaba Buhari ya ke nada Ministocin sa, ya bayar da umurnin su dauki mataimaka daga cikin ma'aikatan gwamnati.

Wannan matsayi da shugaban ya dauka bai zo da mamaki ba, ganin yadda kowa ya san shi da tsattsauran ra'ayi da kuma jajircewa.

Koma bayan da tattalin arzikin ya samu sakamakon faduwar da farashin man fetur ya yi, ya sa dole kasar ta tsuke bakin aljihunta, da kuma dakile duk wata dabi'ar almubazaranci.