An yi `yan tayin Karnuka

Masana kimiyya a jami'ar Conell ta Amurka sun sanar da cewa a karon farko an samu wata Karya da ta haifi 'ya'ya bakwai ta hanyar tagwaita 'yan tayin a kwalba.

Masana kimiyya a jami'ar Conell ta Amurka sun sanar da cewa a karon farko an samu wata Karya da ta haifi 'ya'ya bakwai ta hanyar tagwaita 'yan tayin a kwalba.

An sake mayar da 'yan tayin ne a mahaifar Karyar bayan an tagwaita su.

Masanan sun ce wannan gwajin zai taimaka wajen kare jinsin Karnukan da ke fuskantar gushewa a doron-kasa da kuma irin cututtukan da Karnukan kan gada daga iyayensu.

Sun ce dan tayin Kare zai taimaka wajen nazarin wasu cututtuka da ke damun bil'dama.

Tun a shekarar 1970 da 'yan kai Masana kimiyya suka dukufa wajen tagwaita 'yan tayin Karnuka.