EFCC ta tuhumi Dasuki, Bafarawa da Dokpesi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana tuhumar Sambo Dasuki da karkatar da kudaden da aka ware domin inganta tsaro.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya, EFCC ta tuhumi tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara a kan tsaro Kanar Sambo Dasuki da laifukan da suka danganci almundahana da halasta kudaden haramun a gaban kotu.

EFCC ta kuma tuhumi tsohon gwamnan jihar Sokoto, Dalhatu Bafarawa da mai gidan talabijin na AIT, Raymond Dokpesi, da laifin aikata irin wadannan laifuka a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

EFCC dai ta kama mutanen ne bisa zargin karkatar da kudade fiye da N2.1bn wadanda ke cikin kudaden da aka ware domin sayen makaman da za a yi amfani da su wajen yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.

Sauran mutanen da ake zargi da hannu a wajen raba kudin sun hada da tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda; Shuaibu Salisu, tsohon daraktan kudi na ofishin tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro, da dan gidan Dalhatu Bafarawa, Sagir;

A bangare guda kuma, hukumar ta EFCC tana tuhumar Sambo Dasuki; Shuaibu Salisu; da tsohon darakta a kamfanin mai na NNPC, Aminu Baba Kusa da zargin aikata laifuka 19 da ke da alaka da damfara da karabar hancin da halasta kudaden haram.