An samu galaba a kan Taliban a Kandahar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dakarun Afghanistan a yanzu suke iko da wuraren

Dakarun Afghanistan sun ce, sun yi nasara a kan mayakan Taliban da suka kai hari a kan fararen hula da kuma sansanin soja a yankin Kandahar da ke kudancin kasar.

Ma'aikatar tsaron Afghanistan ta ce, harin yayi sanadiyyar mutuwar fararen hula talatin da bakwai da suka hada da mata da dama da kuma yara kanana.

Wakiliyar BBC ta ce wannan hari shi ne gagarumin matakin kai hare-hare na baya-bayan nan da kungiyar Taliban ta dauka, wadanda cikin watan Satumba suka kwace iko da birnin Kunduz na dan wani lokaci.

An dai kashe tara daga cikin mayakan da suka kai harin.

An kai harin ne da yammacin ranar Talata, lokacin da wasu mayakan na Taliban dauke da manyan makamai suka shiga cikin sansanin sojojin.