Boko Haram: 'An juya wa 'yan gudun hijira baya'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan gudun hijira daga arewa maso gabashin Najeriya.

Tsohon sakataren harkokin wajen Biritaniya, David Milliband, ya bayyana cewa bisa dukkan alamu, duniya ta manta da mawuyacin halin da 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya ke ciki.

Mista Milliband wanda shi ne shugaban Kwamitin kasa da kasa da ke kula da 'yan gudun hijira, watau International Rescue Committe (IRC), ya sanar da hakan ne lokacin da ya ziyarci 'yan gudun hijirar a arewa maso gabashin Najeriya, inda ya ce wajibi ne shugabannin duniya su kara himma wajen taimaka musu.

Ya ce "Yana da muhimmanci sosai mu bayar da rahotanni kan abubuwan da suke a boye, saboda hadari ne a ce abu na faruwa amma ba a san da shi ba, har kuma a manta, sai wadanda babu amfani a sani ne suke fitowa a labarai."

Mista Miliband ya jaddada cewa akwai tashe-tashen hankula da suke a boye a arewa maso gabashin Najeriya, yana mai cewa wasu a da aka dawo dasu daga kasar Kamaru ma suna bukatar taimakon gaggawa.

Kasar Kamaru ta dawo da wasu 'yan gudun hijirar da suka shiga kasarta domin neman mafaka, inda ta ce akwai yiwuwar kasancewar mayakan na Boko Haram din a tsakanin su.

IRC na daya daga cikin kungiyoyin kasa da kasa da ke taimakawa miliyoyin mutanen da ta'addancin Boko Haram ya raba da muhallansu.