Milliband ya koka kan 'yan hijira a Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan gudun hijira a Najeriya

Tsohon Sakataren harkokin wajen Birtaniya ya ce al'umomin kasa da kasa suna mantawa da mawuyacin halin da 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a arewa maso gabashin Nijeriya ke ciki.

Mista David Milliband ya sanar da hakan ne lokacin da ya ziyarci 'yan gudun hijirar a arewa maso gabashin Najeriya.

Ya ce wajibi ne shugabannin duniya su kara himma wajen taimaka wa 'yan gudun hijirar.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da Kamaru ta taso keyarsu zuwa Najeriya sun ce sun sha wahala sosai a hannun jami'an Kamaru.

Wasun su sun ce 'yan gudun hijira suna mutuwa da yawa a Kamaru, sannan suka buka ci gwamnatin Najeriya da ta kai musu dauki.

Wannan dai yana zuwa ne a dai dai lokacin da hukumomi a jihar Borno ke cewa sun fara sake gina garuruwan da sojoji suka kwato daga Boko Haram don bai wa 'yan gudun hijira damar komawa garuruwansu.