Buhari: Za a fara tsugunar da 'yan gudun hijira

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce za a soma mayar da 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu zuwa garuruwansu a shekara mai zuwa.

Shugaban ya yi wannan kalamin ne ranar Laraba lokacin da yake ganawa da tawagar kwamitin bayar da agaji na kasa-da-kasa da ya ziyarce shi a fadarsa da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya shaida wa tawagar - wadda ke karkashin jagorancin tsohon ministan kudin Biritaniya David Miliband - cewa gwamnati za ta sake tsugunar da mutanen wadanda yawansu ya kai miliyan biyu a garuruwansu.

Ya ce gwamnati za ta yi maraba da duk wani taimako da wannan kwamitin da ma wasu kungiyoyi na gida da kasashen waje za su bayar wajen sake mayar da 'yan gudun hijirar cikin hayyancinsu.

Jagoran tawagar Mista David Miliband ya tabbatar wa shugaban na Najeriya cewa kwamitin nasa zai kara kaimi a ayyukan da yake yi, kuma zai taimakawa fiye da 'yan gudun hijirar dubu 350 na jihohin Adamawa da Borno.