An hallaka mutane 37 Kandahar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar Taliban ta kwace iko da wata makaranta, inda ta mayar da ita wurin bude wuta.

Hukumomi a kasar Afghanistan sun ce fararen hula 37 cikin su har da mata da kananan yara ne suka rasa rayukan su a wani hari da kungiyar Taliban ta kai a filin jirgin sama da ke Kandahar.

Rahotanni sun ce har yanzu akwai daya daga cikin mayakan da ake ta fafatawa da shi a cikin filin saukar jiragen saman, a inda sansanin kungiyar tsaro ta NATO da hedikwatar dakarun sojin Afghanistan suke.

Jami'ai sun tabbatar da mutuwar mayakan guda tara.

An kai harin ne da yammacin ranar Talata, lokacin da wasu mayakan na Taliban dauke da manyan makamai suka shiga cikin sansanin sojojin.

Wasu cikin mayakan Taliban din sun kwace iko da wata makaranta da ke kusa da sansanin, inda suka mayar da ita wurin bude wuta, domin agazawa sauran mayakan nasu.