Shin wanene Musulmi ?

A wannan makon 'yan siyasa sun yi wadansu kalamai kan Musulmi da kuma wani martani da aka yi kan harin da aka kai a tashar jirgin kasa a London.

BBC ta tambayi wani ma'aikantanta 11 a kan shin ko su waye Musulmi ana su fahimtar ?

Wanda ke kan gaba a neman tsayawa takarar shugaban Amurka karkashin inuwar jam'iyyar Republican, Donald Trump a wannan makon ya bukaci a haramta wa Musulmi shiga Amurka, bayan da aka kai hari a California.

Wasu ma'aurata Musulmi ne wadanda aka hurewa kunne suka kashe mutane 14 a cibiyar lafiya ta San Bernardino.

'Yan jam'iyyar Republican da na Democrats da shugabannin Musulmi da majalisar dinkin duniya sun yi Allah wadai da wannan kira da suka ce yana da hadari sosai.

Mr Trump ya ce Musulmi na barazana ga Amurka, amma kuma abin tambaya shin ko duka Musulmai ne ke da hadari ?

Ga ra'ayoyin wasu ma'aikatan BBC wadanda suma Musulmai ne.

Musulmi mutum ne wanda ayyukansa da kalamansa ba za su cutar da kowa ba. Musulmi na son zaman lafiya

Mohammud Mohamed, BBC Somali

Musulmi mutum ne da ke nuna dabia ta gari. Annabi Muhammadu ya kasance mai dabiu nagari.

Mohammad Taha, BBC Arabic

Musulmi mutumin kirki ne. Annabi ya shawarci dukkan Musulmai su mutunta tsofaffi tare da kaunar kananan yara.

Mohamed Susilo, BBC Indonesian

Gidanmu mu yan shia ne. Addininmu ya amince da duk Musulmin da ya yarda da Allah daya da manzonsa.

Bahram Farhadtooski, BBC Persian

Musulmi mutum ne da ke nuna kauna ga iyalansa da makwabtansa da kuma abokansa. Mutum ne mai son zaman lafiya wanda ba zai cutar da dan adam ko dabba ba.Kuma ba ya nuna kiyayya.

Aliyu Tanko, BBC Hausa

Musulunci shi ne adalci. Sakon da Annabi Muhammadu ya zo da shi a Kurani shi ne jin kai da zaman lafiya.

Haseeb Ammar, BBC Dari and Pashto

Musulmi mutum ne da ya amince da zamanta kewa da mabiya sauran addinai da aladu tare da mutunta sauran alumma.

Shumaila Jaffery, Wakiliyar, BBC World Service

As a Muslim, I believe God wants me to be happy and hurting others is a direct ticket to a very miserable life. If you try your best to live in peace, you show your love for God.

Margarita Rodriguez, BBC Mundo

Musulmi mutum ne da keda kyakkyawar zato ga wadanda ba Musulmi ba.

Hossein Bastani, BBC Persian

Lokacin ina yar shekaru 9, kakata ta ce min in rufe kai na. Ina kaunar ta amma ba na son Hijabi. Musulmi kamar kaka ce mai kaunar jikarta tare da bukatar a bi sawunta.

Maryam Afshang, BBC Persian

Kasancewa Musulmi shi ne mutunta dukkan alumma ba tare da bambamcin ba.Kuma dole ne a girmama juna.

Fouad Al Chabawi, BBC News