'Ya kamata Buhari ya janye tallafin mai'

Image caption Ana yawan samun layukan mai a Nigeria

Bankin Duniya ya ce yanzu ne lokacin da ya fi dacewa gwamnatin Najeriya ta janye tallafin man fetur, domin kuwa dawainiyarsa ta fi alfanunsa yawa nesa ba kusa ba.

Bankin ya bayyana hakan ne a wani rahoto da ya fitar a kan tattalin arzikin Najeriyar, inda ya ce ana bukatar samun wani sarari ta fuskar kudin shiga domin, kasar ta samu damar sararawa ta samar da muhimman abubuwan da ake bukata.

A cewar bankin, idan Najeriya ta janye tallafin za ta samar da ayyukan yi da kuma kawar da talauci.

Rahoton ya kuma ce masu zuba jari a shirye suke su bude lalitarsu muddin suka ga alamun kudirin sabuwar gwamnatin kasar na samar da manufofin da suka dace da bunkasar 'yan kasuwa masu zaman kansu.

A baya ma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ya bukaci gwamnatin Buhari ta janye tallafi mai amma kuma gwamnatin ta nuna cewar ba tada aniyar janye tallafin man.