Yahoo ya fasa hadewa da kasuwar yanar-gizo ta Alibaba

Kamfanin yahoo Hakkin mallakar hoto
Image caption Kamfanin yahoo

Kamfanin intanet na Yahoo ya fasa hadewa da kasuwar yanar-gizo ta Alibaba

Ana dai danganta mafi yawan hannun-jarin kamfanin Yahoo, wanda ya kai dala biliyon 33 ga kamfanin Alibaba.

Wannan matakin da kamfanin ya dauka ya saba da sanarwar da ya yi a watan Janairu ta hade hannun jarinsa na kashi 15 bisa dari da kamfanin Alibaba.

A yanzu dai kamfanin Yahoo din ya ce zai danka hannun-jarinsa ne ga hannun wani sabon kamfanin hada-hadar hannun-jari.

A shekara ta 2005, Kamfanin Yahoo ya saye kashi 40 bisa dari na hannun-jarin kamfanin Alibaba a kan dala biliyon daya.

Shugabar kamfanin Yahoo Marissa Mayer ta ce kamfanin ya dauki wannan matakin ne saboda ya tabbatar an daraja hannun-jarinsa yanda ya kamata.

A watan Satumban da ya gabata ne aka samu tangarta wajen hadewar kamfanonin sakamakon kin amincewar da mahukunta a Amurka suka yi game da bukatar yin cinikin ba tare da an ciri haraji ba.

Masana harkokin tattalin arziki sun ce wannan warware cinikin zai ba wa kamfanin Yahoo damar sayar da hajarsa ga sauran abokan hulda.