IS na samun miliyoyi a kowanne wata

Kungiyar IS, mai ikirarin kafa daular musulunci, tana samun dala miliyan 80 a kowanne wata, kuma kusan dala miliyan 960 a duk shekara.

A kwanakin nan dai kudaden da ake biyan mayakan IS din ya ragu, inda ta matsa kaimi wurin neman hanyoyin bunkasa tattalin arzikin su.

Kungiyar ta IS ta fito fili ne a duniya a shekarar 2014, lokacin da ta kwace iko da wasu manyan yankunan Syria da Iraki.

Ta yi fice a ayyukan ta'addanci da suka hada da kashe-kashe dayawa a lokaci guda da sace-sacen jama'a da kuma fille kawunan su.

Kungiyar na samu goyon baya daga wasu kasashen musulumi, inda wani hadin kai da Amurka ke jagoranta suka sha alwashin murkushe kungiyar da ake zargi na samun miliyoyin daloli a kowanne wata.

Cikin kudaden da suke samu, kashi 50 cikin dari na zuwa ne daga haraji da suke tilastawa da kadarori da suke kwacewa hannun jama'a.

Kashi 43 kuma daga arzikin man fetur, sauran kuma daga safarar miyagun kwayoyi da kuma sayar da wutar lantarki da kuma gudunmuwa da suke samu.

Image caption Wasu maza da ke sallah gaban shagunan su a birnin Raqqa.

Wakilin BBC, Columb Strack, ya ce kungiyar ta IS dai ba kungiya ce ta ta'addanci kawai ba, yana mai cewa "Tana gudanar da ayyuka ne a matsayin daular da ke zaman kanta, inda suke karbar harajin kashi 20 cikin dari na duk wasu ayyukan kasuwancin da suka hada da masu shaguna da kuma ta intanet".

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban kungiyar ta IS, Abu Bakr al-Baghdadi.

Darektan jami'ar Royal United Services ta kasar Qatar, Michael Stephens, ya goyi bayan cewa ta haka kungiyar ke samun kudaden ta, kuma ya kara da cewa kungiyar ta IS, tana kafa tsarin gwamnati da suka hada da ma'aikatu da kotunan shari'a da kuma ma'aikatar karbar haraji.

Ya ce "Bayan sun kwace iko da gari, sai su yi saurin mamaye ma'aikatun ruwa da kamfanin yin fulawa da kuma matatun man fetur, inda suke mayar da tsarin rabasu waje guda, ta yadda dole mutanen garin su dogara da su domin su rayu".

A watan Satumba ne darektan yaki da ta'addanci na kasa da kasa, watau National Counter terrorism Center (NCTC) Mathew Olsen, ya ce kungiyar ta IS tana iko da yawancin tafkin Tigri-Euphrates, wani yanki da ke da girman mil 81,000, makamancin girman Turai.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu da ake zargin mayakan IS ne tsaye kusa da tutar kungiyar IS kan wani tsauni da ke gabashin Ain al-Arab, wani gari a kasar Syria.

Bayan shekara daya, ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa, dakarun sojin hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta, sun tarwatsa yawancin sansanonin kungiyar ta IS da ke arewaci da kuma tsakiyar Iraki da ma wadanda ke arewacin Syria.

Duk da wannan kalubale da kungiyar ta shiga, sun samu galaba wurin kwace iko da wasu yankuna masu muhimmanci, wadanda suka hada da garin Ramadi da ke yankin Anbar a Iraki da birnin Palmyra da ke yankin Homs a Syria.

Amma duk da miliyoyin dalolin da IS ke samu, kungiyar na fuskantar tsananin takura, hakan kuma ya sa take neman hanyoyin samun kudi, wandanda suka hada da kara kudin haraji ga manoma da kari ga farashin sayar da man fetur ga al'umman Raqqa, domin samun mafita.