Na bai wa Dasuki Naira biliyan 63 — Ngozi

Tsohuwar ministar kudin Najeriya, Dr Ngozi Okonjo-Iwaela na mayar da martani batun karkatar da akalar wannan kudi ba bisa ka'ida ba, ga ofishin tsohon mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro.

Mrs Iweala ta ce kashi 50 cikin 100 na kudaden, ma'aikatarta ta mika wa ofishin tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan tsaro, Kanar Sambo Dasuki watau naira biliyan 63 domin sayen makamai daga cikin kudaden da gwamnati ta kwato, wadanda ake zargin gwamnatin marigayi tsohon shugaban mulkin sojin kasar, Janar Sani Abatcha ta wawure.

Ga rahoton da Badariyya Tijjani Kalarawi ta hada mana

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Karin bayani kan batun'

A wata sanarwar da ta aike wa manema labarai, tsohuwar Ministar ta ce a shekarar da ta gabata ne korafe-korafe suka yi yawa ga tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daga dakarun sojin kasar, kan cewar babu isassun kudaden da yake bai wa wannan bangare dan samar da makaman da za a yaki kungiyar Boko Haram da su a arewa maso gabashin kasar.

Kuma yawanci an yi ta sukar ofishin ta ne kan gazawa wajen samar da wadannan kudade.

Daman dai, a cewarta, aikin ma'aikatar Kudi shi ne samar da hanyoyin da kudade za su shigowa gwamnati wadanda za a yi ayyukan da suka shafi tsaro, da samar da ayyukan yi da ababen more rayuwa kuma abin da ofishinta ya yi kenan.

Ta kara da cewa sai da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya amince da a bai wa Dasuki kudin kafin ma'aikatarta ta tura mishi su.

Tuni dai hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya, EFCC ta tuhumi Kanar Sambo Dasuki da laifukan da suka danganci almundahana da halasta kudaden haramun a gaban kotu.

EFCC ta kuma tuhumi tsohon gwamnan jihar Sokoto, Dalhatu Bafarawa da mai gidan talabijin na AIT, Raymond Dokpesi, da laifin aikata irin wadannan laifuka a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

EFCC dai ta kama mutanen ne bisa zargin karkatar da kudade fiye da N2.1bn wadanda ke cikin kudaden da aka ware domin sayen makaman da za a yi amfani da su wajen yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.