Assad: 'Yan tawayen Syria sun hada kai

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption 'Yan tawayen Syria sun hade kai gabanin tattaunawa da gwamnatin shugaba Bashar al Assad

Kungiyoyin 'yan adawa a Syria sun yi muwafaka a kan wasu jerin bukatu da za su gabatar gabanin tattaunawar da za a yi da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

A karshen wani taro da aka yi a Saudiyya, sun yi kira da a dauki matakan da zasu sa a samu yarda da juna gabanin duk wata tattaunawa.

Bukatun nasu sun hadar da sakin fursunoni da ke gidan yarin gwamnati da kuma sassauta kofar ragon da aka yi wa yankunan da ke hannun 'yan tawaye.

Kafin a kai ga cimma yarjejeniyar karshe a taron, wani bangaren 'yan tawaye da ake kira Ahrar al-Sham ya fita daga wajen.

Bangaren ya yi korafin cewa mutanen da suke ganin suna kusa da gwamnati sosai su su ke ruwa da tsaki a taron.