An kai hari barikokin sojin Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Burundi ta fada rikici tun lokacin da Pierre Nkurunziza ya ce zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku.

Wasu mahara dauke da manyan makamai sun kai hare-hare a barikokin soji daban-daban da ke Bujumbura, babban birnin Burundi.

Ganau sun bayyana cewa sun kwashe awowi da dama suna jin karar harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa.

Rahotanni na cewa an kashe da dama daga cikin maharan.

Wani mai bai wa shugaban kasar Pierre Nkurunziza shawara ya ce masu hamayya da gwamnati na yin yunkurin tayar-da-zaune-tsaye a kasar, amma ba sa yin galaba.

Kasar dai ta fada cikin rikici ne tun a watan Aprilu, lokacin da Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku, sabanin yarjejeniyar da aka kulla.