'Yan bindiga na ci gaba da kai hare hare

Rundunar sojin Najeriya, ta ce wani ayarin dakarunta dauke da kayan abinci ya gamu da koma-baya a kan hanyar Bama da Ngurosoye da ke jihar Borno a ranar Alhamis.

Ta ce wasu 'yan bindiga suka yi wa ayarin kwanton-bauna, inda kuma aka kashe soja daya da farar-hula guda.

Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa a kalla mutane 14 aka kashe a wani hari da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kaiwa wasu kauyuka biyu da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya

Ana samun hare-haren 'yan bindiga a daidai lokacin da wa'adin da aka diba wa wa sojoji na dakile boko-haram ke cika

.