Kaduna: Buhari ya halarci taron mawaka

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya halarci taron da gwamnatin jihar Kaduna da hadin gwiwar wasu cibiyoyi masu zaman kansu suka shirya domin sakawa wasu makawa da suka goyi bayan jam'iyyar APC.

Ana gudanar da wannan taro na kalankuwar wakoki da rawa ne a babban filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna, inda makawa daga kudu da kuma arewacin Nigeria zasu cashe.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa'i ya ce, an shirya taron ne da hadin gwiwa da wasu cibiyoyi masu zaman kansu, domin nuna godiya ga mawakan da kuma rawar da suka taka a zaben da ya gabata.

Amma tuni wasu 'yan siyasa da kuma malaman addini suka soki lamarin, suna cewa, ganin irin halin da talakan Najeriya yake ciki bai kamata a yi irin wannan taro ba na sheke aya.