Zaɓen Saudiyya: Mata suna jefa ƙuri'a

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Karon farko a Saudiyya mata suna kada kuri'a a zaben da ake gudanarwa.

An kuma baiwa matan damar tsayawa takara a zaben na gundumomi da ake yi a duk fadin kasar.

Kusan mata dubu ne suka tsaya takara, da kuma maza kusan dubu shida.

Amma an gindaya iyaka dangane da yakin neman zabe, inda aka haramtawa mata 'yan takarar neman kuri'ar maza kai tsaye, ko ido-da-ido.

A Saudiyya dai an haramtawa mata tukin mota.