An kashe mutane 15 a birnin Homs

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mutane 15 sun mutu a Homs

Rahotanni daga birnin Homs a Syria na cewa an kashe a kalla mutane goma sha biyar yayin da wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari da aka kai da mota.

Wani da abin ya faru a idonsa ya ce harin ya munana matuka gaya, kuma ana ganin sassan jikin mutane a warwatse a kan kasa.

Harin ya zo ne kwana guda bayan an fara amfani da yarjejeniyar fahimtar junan da aka cimma tsakanin 'yan adawa da kuma bangaren gwamnati a Syria.

A karkashin yarjejeniyar, daruruwan mayakan 'yan adawa za su bar birnin na Homs sannan dakarun gwamnati za su kara tsaurara tsaro da kuma iko da birnin.