An hallaka mutane 87 a Burundi

Gawar wani dan Burundi da aka kashe a kasar
Image caption Gawar wani dan Burundi da aka kashe a kasar

Sojoji a Burundi sun ce mutum 87 aka kashe a rikicin da aka yi ranar Juma'a a babban birnin kasar, Bujumbura, kuma takwas daga cikinsu Sojoji ne.

Wakilin BBC ya ce wannan ce asarar rayukan jama'a mafi muni, tun lokacin da kasar ta fada cikin rikicin siyasa.

Ya kuma ce a gundumar daya kadai ya kidaya gawakin mutum 21 a kan tituna da gidaje.

Ya ce wannan dai shi ne karon farko da wadannan mutane suka kai hari kan sojoji jiya, kuma ita ce rana mafi muni ta fuskar mutuwar jama'a tun lokacin da aka fara wannan rikici a Bujumbura.