An soma shari'a kan juyin mulki a Burundi

Janar Ndayirukiye ya ce ana kuntata masa a kurkuku
Bayanan hoto,

Janar Ndayirukiye ya ce ana kuntata masa a kurkuku

Ana tuhumar tsohon ministan tsaron Burundi, Janar Cyrille Ndayirukiye da wasu tsaffin jami'an tsaro su 30 bisa zarginsu da hannu a yunkurin yi wa shugaba Pierre Nkurunziza juyin mulki.

Sun bayyana a gaban kotu, inda suka ce an ajiye su a cikin dan karamin daki cikin yanayi na rashin tausayi.

An yi yunkurin juyin mulkin ne, 'yan makonni bayan da shugaba Nkurunziza ya bayyana cewar zai tsaya takara a karo na uku, duk da cewar kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa.

Kusan mutane 90 aka kashe a ranar Juma'ar da ta gabata, a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari a gine-ginen gwamnati.

Tun daga watan Afrilun bana an tsare daruruwar mutane a yayin da ake ci gaba da shiga rashin tabbas a kasar.