Shi'a:'Ba mu san inda El-Zakzaky yake ba'

Hakkin mallakar hoto MEHR
Image caption El-Zakzaky ya musanta ikirarin sojojin Nigeria

Kungiyar Islamic movement ta 'yan Shi'a a Nigeria ta ce kawo yanzu ba ta san inda shugabanta, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky yake ba.

Hakan dai ya biyo bayan samamen da sojoji suka kai ne a gidansa da ke Gyallesu a Zariya da kuma wasu wuraren ibada na 'yan shi'a da ke birnin.

Sanarwar kungiyar dauke da sa hannun, Ibrahim Musa ta ce ba su san inda El-Zakzaky yake ba ko kuma halin da yake ciki ba amma dakarun Nigeria sun kama shi a ranar Litinin da safe.

Wata diyar Sheikh Ibrahim Al Zakzaky, mai suna Suhaila ta shaida wa BBC cewa ba ta da masaniya game da inda aka tafi da mahaifinta.

Tuni dai 'yan Shi'a din suka ce an kashe Malam Muhammadu Turi da matar El-Zakzaky, Malama Zeenatu da dansa, Sayyid Ali.

'Yan shi'ar sun kuma ce, an kashe da dama daga cikin mabiya mazhabar ta Shi'a, sannan aka rusa gidan jagoran nasu.

'Maido da doka'

Sojojin kasar sun zargi kungiyar ta Shi'a da yunkurin halaka babban hafsan sojin kasar lokacin da yaje Zaria ranar Asabar, sai dai kungiyar ta musanta wannan zargi.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An dade ana zargin sojojin Nigeria da take hakki bil adama

A cikin wata sanarwa da Kanar Sani Usman Kukasheka ya fitar, rundunar sojin ta tabbatar da asarar rayuka, amma ba ta yi karin bayani ba ko mutane nawa ne suka mutu, ko kuma daga wanne bangare.

Sanarwar ta kuma ce, da zarar an maido da doka da oda a garin Zaria, 'yan sanda za su gudanar da bincike domin gano abinda ya faru.

Ana dai ci gaba da zaman dar dar a Zaria, sakamakon arangama tsakanin Sojojin da kuma yan kungiyar ta Shia.

Kasar Iran - wacce ke goyon bayan kungiyar Shi'a a Najeriya - ta yi kiran a kwantar da hankali.