"Za mu ba El-Zakzaky damar magana nan gaba"

Hakkin mallakar hoto non
Image caption Sheikh Ibrahim Zakzaky

A Najeriya hukumomin Sojin kasar sun ce nan gaba za su ba shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi a kasar, Sheikh Ibrahim Zakzaky dama ya yi magana da mabiyan sa.

Shugaban rundunar sojin a Kaduna, Manjo Janar Oyebade wanda ya sanar da hakan ga manema labarai ya ce, a yanzu haka shugaban kungiyar ta Islamic movement, Malam Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Malama Zeenat na hannun jami'an tsaro kuma suna cikin koshin lafiya.

A ranar Lahadi ne, kungiyar ta 'yan Shi'a ta bayyana cewar an hallaka Malama Zeenat tare da wasu manyan shugabannin kungiyar kamar, Malam Turi da kuma Malam Ibrahim Usman.

Ana ci gaba da zaman zullumi a yankin Gyallesu inda gidan El-Zakzaky yake a birnin Zariya a yayin da kuma ake zargin jami'an tsaron sun hallaka mabiya kungiyar da dama.

Sojojin kasar sun zargi kungiyar ta Shi'a da yunkurin halaka babban hafsan sojin kasar lokacin da ya je Zaria ranar Asabar, sai dai kungiyar ta musanta wannan zargi.