Kotu ta yanke wa Hadiza Bawa-Garba hukunci

Image caption Dr Hadiza Bawa-Garba da Isabel Amaro ba za su yi zaman jarun ba

Kotu a Ingila ta yanke wa Dr Hadiza Bawa-Garba, daurin hukuncin je ki gyara halinki na shekaru biyu, saboda samun ta da laifin kisan kai bada niyya ba.

Haka kuma kotun ta yanke wa Isabel Amaro hukunci iri daya da Dr Hadiza, saboda samunsu da sakacin aiki abin da ya janyo rasuwar Jack Adcock, dan shekaru shida a wani asibiti da ke birnin Leicester.

A lokacin yanke hukuncin, mai shari'a Andrew Nicol ya ce sakacin ma'aikatan asibiti su biyu ya janyo "mutuwar Jack cikin kankanin lokaci".

Jack Adcock wanda ke fama da ciwon maloho da kuma matsalar zuciya, ya rasu ne a wani asibiti da ke Leicester a watan Fabarairun 2011.

Dr Hadiza Bawa-Garba 'yar asalin Nigeria ce, iyayenta ne suka turo ta Ingila karatu kuma ta samu shaidar zama likita a makarantar koyan aikin likita ta Leicester Warwick.