Mun zafafa kai hare hare kan IS - Obama

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Obama ya ce sojojin kawance sun zafafa kai hare-hare kan kungiyar IS sai dai akwai bukatar samun nasara cikin gaggawa.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a shalkwatar tsaro ta Pentagon, ya kuma kara da cewa "ce an kaddamar da hare-hare masu yawa akan kungiyar ta IS din ne a watan Nuwamba fiye da kowanne wata"

Shugaban na Amurka ya kara da cewa. 'Yan kwanakin nan hare-haren da Amurkan ke jagoranta kan kungiyar IS din sun halaka da yawa daga cikin shugabaninta baya ga lalata wuraren hakar mai inda kungiyar ke samun kudin shiga.

Mista Obama ya kuma ce kungiyar IS ta yi hasarar kimanin kashi 40 na adadin inda ta ke rike da shi a Iraqi, kuma kungiyar ba ta sake samun nasara ba a Iraqi da Syria.

Cikin wadanda aka hallaka a hare-haren da sojojin kawancen suka kai na bayan bayan nan a cewar Obaman sun hada da Mohammed Emwazi wanda aka fi sani da John Jihadi wani dan wani Britaniya haifuwar Kuwati wanda ya rika fitowa a hotunan bidiyo yana kisan wasu turawan yamma da IS din ta kama.