Rwanda: An yanke hukunci na karshe

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An samu Pauline Nyiramasuhuko da laifin kisa

Kotun Duniya ta Miyagun Laifuka a kan Rwanda ta yanke hukuncinta na karshe, a kan wadanda ke da hannu a kisan kare-dangin da aka yi a 1994.

An kafa kotun ne a 1995 bayan kisan gillar.

Yanzu kotun, a birnin Arusha ta Tanzania, yanzu za a rusa ta.

An samu duka mutane shida da laifi, amma an rage hukuncin uku daga cikinsu daga daurin rai da rai zuwa shekaru 47 a gidan kaso.

Sai dai yayin da wasu da dama ke yabon aikin kotun, wasu suna sukar ta bisa cewa aikin nata bai kai yadda ya kamata ba.

Cikin shekaru 20 din da aka kafa ta samu mutane sittin da daya da aikata laifin.