Kano za ta gina kasuwar fina-finai

Image caption Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Ganduje yayi alkawarin ci gaba da taimakawa 'yan fim domin su ci gaba da samar da aikin yi

Gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya ta ce za ta gina babbar kasuwar zamani ta sayar da fina-finai.

Kwamishinan yada labarai na jihar Mohammed Garba ne ya sanar da hakan a lokacin da ya ke jawabi ga masu sana'ar shirya fina-finan da suka kai masa ziyara a ofishinsa.

Kwamishinan ya kara da cewa shirye shirye sun yi nisa dangane da soma ginin kasuwar a shekara mai zuwa wacce tuni har an fitar da taswirar gininta.

Jihar Kano ita ce cibiyar shirya fina-finan Hausa wanda aka fi sani da Kanywood wacce ta yi fice a ciki da kuma wajen Najeriya.

An kiyasta cewa masana'antar shirya fina finan ta Kanywood na samarwa matasa sama da milyan daya aikin yi.

An yi hasashen cewa kasuwar za ta habaka sana'ar da kuma karin ayyukan yi a Kano da kuma Arewacin kasar idan aka shawo kan matsalar satar fasaha wacce ta addabi masana'antar.