'Za a kara kudin mai a 2016 a Nigeria'

Image caption Ana yawan fuskantar karancin mai a Nigeria

Gwamnatin Nigeria na shirin soma janye tallafin man fetur daga shekara mai zuwa.

Minista a ma'akatar harkokin man fetur, Dr Ibe Kachukwu shi ne ya sanar da haka a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin hadaka na majalissun dokokin Nigeria domin ya kare kasafin kudin ma'akatarsa.

A cewarsa, a bana an kashe fiye da naira tiriliyan daya a tallafin mai kuma wannan dawainiya ce da gwamnatin ba za ta iya ci gaba da dauka ba.

Ministan ya kara da cewar za a janye tallafin da kadan-kadan inda da farko za a kara kudin mai ya koma naira 97 kowacce lita daga farashin da yake a yanzu na naira 87 kowacce lita.

Masana harkokin tattalin arziki a Nigeria da kasashen waje sun dade suna kira ga gwamnatin kasar ta janye tallafin man fetur saboda a cewarsu dawainiyarsa ta fi alfanunsa yawa.