Rouhani ya kira Buhari saboda El-Zakzaky

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Iran ta bukaci a gudanar da bincike kan lamarin

Shugaban Iran, Hassan Rouhani ya kira shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ta wayar tarho domin nuna korafinsa a kan kashe 'yan Shi'a da sojoji suka yi.

Kafafen yada labarai a Iran sun ruwaito cewar Rouhani ya kira Buhari ne domin bayyana masa cewar "ka da karamar matsala ta zama babba" a tsakanin Musulmai.

Mr Rouhani ya kuma nemi karin bayani kan makomar shugaban 'yan Shi'a, Malam Ibrahim El-Zakzaky bayan da sojoji suka kama shi a gidansa sannan kuma suka rusa gidan.

Shugaban Iran din kuma ya bukaci a gudanar da bincike kan lamarin.

Kungiyoyin kare hakkin bil-adama a Nigeria sun ce an kashe 'yan Shi'a sama da 200 a lokacin da sojojin suka diranma gidan El-Zakzaky da kuma Husainiyya a Zariya.

Koda yake dai sojojin sun musantan adadin wadanda suka rasu, amma dai sojojin basu bayar da alkaluman kan wadanda aka kashe ba.

Rikicin ya samo asali ne bayan da sojoji suka yi zargin cewar 'yan Shi'a sun yi yunkurin hallaka babban hafsan sojin kasar lokacin da ya je Zaria a ranar Asabar, sai dai kungiyar ta musanta wannan zargi.