'Yan Shi'a na muzahara a arewacin Nigeria

Daruruwan 'yan Shi'a a wasu garuruwan arewacin Nigeria suna gudanar da muzahara domin nuna adawa da matakan da sojoji suka dauka a kan 'yan kungiyar a Zariya.

Rahotanni sun ce mabiya shi'a sun zanga-zanga a Kaduna da Kano da Sokoto da Bauchi da kuma Zamfara.

Bayanai sun ce 'yan Shi'a sun bazama a kan wasu tituna a garin Kaduna inda suke korafi kan irin yadda abubuwa suka kasance bayan da sojoji suka kama shugaban 'yan Shi'a, Malam Ibrahim El-Zakzaky tare da wasu mabiyansa.

Rahotanni sun ce an baza jami'an tsaro a wasu manyan tituna da ke Kaduna domin hana afkuwar rikici.

A yanzu haka dai an rufe shaguna da wasu manyan ofisoshi a Kaduna a yayin da aka soma zaman dar-dar.

Can ma a birnin Kano, bayanai sun ce 'yan Shi'a na gudanar da muzahara saboda abin da suka kira muzgunawar da sojojin Nigeria suka yi musu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Malam Imam Kurna shugaban 'yan shi'a a Kano ya yi wa wakilinmu, Yusuf Ibrahim Yakasai karin bayani kan dalilin zanga-zangarsu

Tun bayan da aka soma rikici tsakanin sojoji da 'yan Shi'a a Zariya, bayanai sun ce an hallaka mutane da dama sannan kuma an rusa wuraren ibada na 'yan Shi'a din a Zariya.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a Nigeria sun yi zargin cewa an hallaka 'yan Shi'a fiye da 200 a lokacin da sojojin suka kai samame a gidan El-Zakzaky a karshen mako a Zariya.