Syria: Amurka da Rasha za su hada kai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jiragen yakin Rasha na lugude a Syria

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce yana san rage bambance-bambancen da ake da su tare da Rasha a game da yadda za'a kawo karshen yakin basasar Syria.

Yanzu haka Mr Kerry yana Moscow, inda yake ganawa da takwaransa na Rashar, Sergei Lavrov.

Daganan kuma zai tattauna na shugaba Putin.

Duka bangarorin biyu sun amince su yaki kungiyar 'yan bindiga ta IS.

Mr Kerry ya ce "a game da ISIL ko Daesh, Rasha da Amurka sun amince da cewa wata babbar barazana ce ga kowa ga duka kasashe."

Sai dai Rasha da Amurka ba su amince a kan wadane kungiyoyin 'yan tawayen Syria ne za'a gayyata zuwa taron da za'a yi a watan Janairu, da kuma rawar da shugaba Basharul Assad zai taka a siyasar kasar.