Ban karbi kudi daga wajen Dasuki ba — Buhari

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana zargin Sambo Dasuki ya sace kudin da aka ware domin sayen makamai.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karyata rahotannin da ke cewa ya karbi $300,000 da motoci biyar masu sulke daga wajen Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasar shawara a kan tsaro.

Rahotannin dai na cewa Shugaba Buhari ya karbi kudi da motocin daga wajen Dasuki ne sakamakon harin da aka kai masa a Kaduna a shekarar da ta wuce, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma lalata motar da yake ciki.

A wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan watsa labarai, Femi Adesina ya fitar, ya ce ko da ya ke shugaban ya karbi mota daya mai sulke da kuma mota maras sulke bayan harin, amma dokar kasar ce ta bukaci a ba shi su a matsayinsa na tsohon shugaban kasa a wancan lokacin.

Sanarwar ta kara da cewa, "Don haka muna sanar da cewa Shugaba Buhari bai karbi $300,000.00 ko kuma duk wani kudi da nufin karbar diyya daga wajen tsohon shugaba Jonathan, ko kuma duk wani jami'in gwamnatinsa, bayan harin da aka kai kan tawagarsa".

Mista Adesina ya ce "Buhari ya karbi motar da aka ba shi ne saboda sashe na uku, karamin sashe na daya na kundin tsarin mulkin Najeriya da ke bayani kan abubuwan da suka kamata a bai wa tsofaffin shugaban kasa, ya bukaci a ba shi motocin. Don haka bai karya wata dokar kasa ba".

A cewarsa, babu wanda ya isa ya ruguza martaba da kimar da shugaban kasar yake da su, saboda tun da yake ba a taba samunsa da aikata laifuka, musamman na karbar hanci da rashawa ba.