Facebook zai sauya dokar yin amfani da "suna"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Facebook ya sha suka saboda rashin bai wa mutane damar yin amfani da sunayen da ba nasu ba.

Shafin sada zumunta na Facebook ya ce zai sauya dokar da ya kafa cewa dole duk wanda zai yi rijista da shafin sai ya yi amfani da sunansa na gaskiya.

Shafin dai ya sha suka daga wajen mutane daban-daban a kan wannan batu, inda suke cewa akwai bukatar a sauya dokar domin bai wa mutanen da ake tsangwama damar yin rijista da sunayen bogi domin su samu damar fallasa cin zarafin da ake yi musu ba tare da an gane su suka yi hakan ba.

Facebook ya ce zai yin gwajin wadansu sababbin manhajoji da za su bai wa mutane damar fadar dalilan da suka sa ba za su rika yin amfani da sunayensu na gaskiya ba.

Facebook ya kare matakinsa na son masu amfani da shi su yi rijista da sunayensu na ainihi, yana mai cewa hakan zai sa mutane su rage yin katobara wajen yin amfani da shafin.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama ne dai suka rika sukar Facebook domin ya bai wa mutanen da ake musgunawa damar boye sunayensu a shafin, ta yadda za su fallasa mutanen da ke cin zarafinsu ba tare da jin tsoro ba.