'Yan bindiga sun sace 'yan Qatar 27

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kasa samun zaman lafiya a Iraki

Hukumomi a Iraki sun ce 'yan bindiga sun sace 'yan kasar Qatar su 27, ciki har da 'yan gidan sarauta, a wani sansanin farauta.

Hukumomin sun ce 'yan bindigar cikin manyan motoci sun sace mutanen ne a wani gari da ke kan iyakar Iraki da Saudiyya.

Garin na karkashin ikon 'yan Shi'a.

Jam'iyyun 'yan Shi'a a Iraki na sukar gwamnatin Qatar saboda goyon bayan 'yan mazhabar Sunni a Syria.

Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce tana aiki tare da gwamnatin Iraki domin a sako 'yan kasar ba tare da bata lokaci ba.