'Yan Boko Haram mata sun mutu a Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno na cewa, wasu daga cikin 'yan mata 'yan kunar bakin wake biyar da suka yi yunkurin shiga Maiduguri ta hanyar Mafa sun halaka kansu.

Harin kuma ya janyo mutuwar wasu 'yan sintirin tsaro na sa kai, watau Civilian JTF.

Lamarin dai ya auku ne a shingen binciken tsaro na kan hanya.

Daga bisani dai sauran 'yan matan da shekarunsu basu wuce tara sun mutu yayin da ake kokarin kwance bam din da ke jikinsu.

Sanyawa mata bam na kunar bakin wake dai na daga cikin sabbin salon da kungiyar Boko Haram ta bullo su.

Alhaji Muhammed Kanar, shi ne jami'an hukumar agajin gaggawa ta NEMA a jihohin arewa maso gabas.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ta waya ya yi wa Isa Sanusi karin bayani akan abinda ya faru: