An gano gawarwaki 19 a Mexico

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hotunan wasu daliban da suka bace a Mexico

An gano gawarwakin akalla mutane 19 a jihar Guerrero ta kasar Mexico, inda wasu dalibai 43 suka bace a bara.

'Yan sanda sun ce an jefa gawarwakin ne a wata hanyar ruwa a bayan gari, kuma duwatsu da bishiyoyi suka rufe su.

Takwas daga cikin gawarwakin an kona wasu sassa na su.

'Yan sanda sun ce bincike da suke gudanarwa a kan wasu bayanai da suka samu ne, ya kai su ga gano gawarwakin.

Ana sa rai za a yi wa gawarwakin gwajin kwayar halitta don kwatanta su da na iyalai fiye da 600 da suka ce 'yan uwansu sun bace.

Alkaluman gwamnati sun nuna cewa fiye da mutane 650 ne aka kashe bara a Guerrero, daya daga cikin jihohi da suka fi samun tashe-tashen hankali a Mexico inda kungiyoyin masu sayar da miyagun kwayoyi suka yawa.