'Yan gudun hijira 1,187 sun dawo daga Kamaru

Image caption Hukumar NEMA ta ce tana sa ran kara karbar 'yan gudun hijira 15,000 nan gaba

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce ta karbi 'yan gudun hijira 1,187 da suka hada da mata da yara daga jamhuriyyar Kamaru.

Hukumar ta ce ta karbi mutanen ne a sansanin 'yan gudun hijira na Fufore a jihar Adamawa tsakanin ranakun Litinin zuwa Laraba.

A wata sanarwa da ta fitar wadda kakakin kungiyar Sani Datti ya sanyawa hannu, NEMA ta ce jami'an hukumar da na kungiyar Red Cross wadanda suka karbi 'yan gudun hijirar sun tantance 'su tare da yi musu rijista.

Sanarwar ta kara da cewa tuni aka bai wa 'yan gudun hijirar masauki da abinci da dukkan abubuwan bukata.

Ana sa ran kimanin 'yan gudun hijira 15,000 ne za su dawo Najeriya daga Kamaru cikin makonni kadan masu zuwa.

'Yan gudun hijirar 'yan Najeriya ne wadanda suka tafi Kamaru don neman mafaka sakamakon rikice-rikicen kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.