An amince da ranar zabe a Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Manyan 'yan adawar Nijar

Gwamnatin Nijar ta amince da ranar 21 ga watan Fabarairu a matsayin ranar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.

Haka kuma gwamnatin ta ce a ranar, za a yi zaben 'yan majalisar dokoki a yayin da za a soma kamfe daga ranar 30 ga watan Janairu zuwa 19 ga watan Fabarairu.

Shugaba Mahamadou Issoufou wanda ya lashe zabe a shekarar 2011, yana neman takara a karo na biyu.

Babban mai kalubalantar shugaban, shi ne tsohon Firai minista Seyni Oumarou, wanda ya zo na biyu a zaben 2011.

Shi ma tsohon kakakin majalisar dokoki, Hama Amadou yana takarar shugabancin kasar.