Ana juyayin mutanen da aka kashe a Peshawar

Image caption Dalibai su ne harin ya fi shafa.

A kasar Pakistan, an yi tarukan nuna juyayi domin tunawa da 'yan makaranta kusan 150 da 'yan bindiga suka kashe a Peshawar shekara guda da ta wuce.

Firai Ministan kasar, Nawaz Sharif, ya gaya wa mahalarta taron cewa harin da 'yan kungiyar Taliban suka kai a makarantar sojoji ya "girgiza kasar".

Malamai da daliban da suka tsira daga harin sun yi jawabi kan halin da suka shiga a lokacin.

Wasu daga cikin daliban sun ce suna bukatar karin magunguna da kuma rarrashi domin su manta da lamarin.

A birnin Lahore, an dakatar da tafiye-tafiyen abubuwan hawa na minti biyu, haka kuma masu gabatar da shirye-shiye a gidan talabijin din Geo mai zaman kansa sun sanya irin kayan makarantar sojojin domin bayyana alhininsu.

Gwamnatin kasar ta ce za ta sauya sunan makarantar zuwa sunayen mutanen da harin ya shafa domin karrama su.