Shin ana son abincin Afrika a London?

  • Daga Carinya Sharples da Geneviève Sagno
  • Ma'aikatan BBC Africa

Idan kai mazaunin kusa da kasuwar Adjame ne a birnin Abidjan, ko kasuwar Dantokapa a birnin Cotonou, ko babbar kasuwar Ouagadougou ko ta Alaba a Lagos, to ka san cewa wurare ne da saye da sayarwa ke tafiya ba kama-hannun-yaro, idan aka yi la'akari da yadda ake lodin kayan abinci, kamar su doya da agada da rogo da sauransu.

'Yan Afrika mazauna London na iya samun dukkan nau'in abincin da suke kewa irin na kasarsu.

Amma a yau, dukkan kasuwannin da ake samun nau'o'in abincin Afrika sun ja da baya.

Mun yi kira ga abokanmu aikinmu na sahsen BBC Afrika da su yi nazari kan kasuwannin da suka fi yin tashe a London.

Daga jerin sunayen kasuwanni biyar da aka zayyano, bari mu ga wadanne ne har yanzu suke da abin da za a yi rubutu a kansu:

Kasuwar gefen titin Ridley

Ayyukan bunkasa kasuwa ya jawo ce-ce-ku-ce a London, inda masu sukar lamiri ke cewa ya sauya yanayin birnin. Kasuwar gefen titin Ridley da ke gabashin London ta guji irin haka. Waje ne da ya kunshi inda matasa da tsofaffi da masu kudi da ma'aikata ke fadi tashin sayen nau'o'in abincin Afrika da kayaan kawa.

Asalin hoton,

Bayanan hoto,

Doya da dankali da gwaza na da farin jini a London

A kasuwar gefen titin Ridley ko kasuwar Dalston kamar yadda aka fi saninta, ana samun busasshen kifi da agada da gujjiya da duk wani nau'in abincin Afrika ta yamma.

Wakiliyar BBC Genevieve Sagno ta ce, "A duk lokacin da 'yan uwana suka zo na kuma ji son dafa musu abincin Afrika, na kan je kasuwar Dalston. Mahaifiyata na matukar son busasshiyar kaguwa don karawa miya dandano. Abin da kawai za ka yi shi ne neman inda ake sayar da abin da ka ke nema kuma tabbas za ka samu."

Akwai ma wani nau'in abincin Ivory Coast 'l'attiéké', wanda ake yin sa da rogo.

Genevieve ta ce "Ana cinsa ne da tumatur ana kuma nade shi cikin bawon ayaba, yana da matukar dadi."

A cewarta kasuwar gefen titin Ridley tana da dogon tarihi tun shekarun 1800.

A wancan lokacin akwai kimanin rumfuna 20, amma a yanzu akwai kusan rumfuna 200. A shekarar 2012 ne BBC ta yi wani bincike a boye wanda ya gano ana sayar da naman dawa ba bisa ka'ida ba kamar su ........

Kasuwar naman dawa ta Shepherd

An samar da aksuwar naman dawa ta Shepherd a yammacin London tun farkon karnin da ya gabata, kuma in dai kana neman nau'o'in kayan abincin Afrika ne, to lallai je ka wannan kasuwar.

Wakiliyar BBC Veronique Edwards ta ce "Ina iya tunawa a lokacin da na fara zuwa London a shekarun 1970, a kasuwar naman dawo ta Shepherd ne kawai za ka samu duk kayan abincin Afrika da ka ke nema. Amma yanzu kana iya samun abincin Afrika a ko ina har ma da manyan kantuna."

Kasuwar Shepherd na cikin yankin wani babban rukunin shaguna na Westfield, wanda ya bude kofofinsa shekaru biyar da suka gabata. Hakan ya jawo abokan ciniki kara tururuwar zuwa wajen.

Veronique ta kuma kara tunawa cewa, "Waje ne na ganawa, waje ne da za ka hadu da abokai a ranakun Asabar ko Lahadi, har ku shirya kai wa juna ziyara, a can ne kuma ka ke sanin su waye suka zo London. Ka tuna fa cewa duk wannan na faruwa ne kafin samuwar wayoyin hannu, kuna iya koyawa juna girki, kamar me ya kamata ka yi amfani da shi a madadin wani sinadarin girki da baka samu ba. A takaice dai haduwa a wajen na sa ka kara samun haske kan abubuwa da dama."

Kasuwar Brixton

Wata babbar kasuwa da a baya babu wacce ta kai ta fice a Turai wajen samun abincin yankin Caribbean ita ce kasuwar Brixton, a yanzu kuma ta fi jan hankalin matasa 'yan bana bakwai, saboda kantunan cin abinci masu sanya nishadi da mashaya da ke cikinta, inda a yanzu ta zamo kamar rufaffiyar kasuwa.

Amma ga mai son sayen kayan abincin Afrika, to kasuwar Brixton ma wajen lekawa ce.

Za ka samu rumfuna da aka jere agada da kubewa da danyen kifi da nama kala-kala da kayan kanshi, da kayan abinci da sauransu. Kuma wasu masu girke-girken abincin Afrika sun samu sabuwar aksuwa ta dafa nau'o'in abincin Afrika kala-kala, kamar su kantin abinci na Zoe da ake girka abincin Ghana da Kata Kata da ake sayar da abincin Kamaru da sauransu.

Kasuwar Waamo

Ma'aikacin sashin Somali na BBC, Ahmed Abdinur ya ziyarci rukunin shagunan kasuwar Waamo, wacce ke yammacin London, kuma a shekaru uku da suka wuce kasuwar na da farin jini.

"Babbar kasuwa ce wacce ake sayar da kayan sawa, da abinci da abubuwa da dama, kuma mutane na zuwa sosai. Galibin 'yan Somalia na zuwa."

Sai dai abin mamaki a yanzu kasuwar ta rame, sai dai shaguna kadan kuma babu jama'a sosai. "Shin me ya faru ne? in ji Ahmed. "Muna amfani da kayayyakin abinci na 'yan Italiya domin yin abincin 'yan Somalia kamar taliya da biredi da shinkafa da sauransu."

Kasuwar Queens (Sarauniya)

Ba duka kasuwannin bane ke canzawa. A kasuwar Queens wacce ake kira Upton Town Market - 'yan Afrika daga kasashe daban-daban na zuwa. "'Yan Ghana da Najeriya da Kamaru da Congo da Saliyo..duk suna zuwa," in ji Josephin Hezeley wacce ke zuwa siyayya a kasuwar. "Akwai manja da Kwe Kwe da Agushi da Dodo da Fufu."

Asalin hoton,

Bayanan hoto,

Tsofaffi ma zuwa kasuwar domin siyyaya

An gina kasuwar Sarauniya a shekarar 1904. Kuma tun daga lokacin an gabatar da shirye-shirye kan abinci a BBC daga kasuwar sau da dama.

Ga ma'aikatan sashin Swahili na BBC a London, akwai abinci iri-iri na kamar gwaza da rogo da dankali da doya da kuma kwakwa," in ji Zuhura Yunus ta BBC Swahili.

Ga 'yan Afrika da ke zaune a London, kasuwanni na basu damar sayen kayayyakin abincin da suka sama ci a gida kuma a farashi mai rahusa.

Dandalon Abincin Gida, wani shiri na BBC a kan Abincin Afrika wadanda ake samu a kasashen waje.