Taurarin Bollywood sun fi na Star Wars kasuwa

Hakkin mallakar hoto Red Chillies Entertainment
Image caption Fim din Dilwale, shi ne aka fi kashewa kudi a bana

Wannan makon ya kasance makon da ake dakon fitowar fim din Star Wars.

A ranar 18 ga wannan watan ne fim din Star Warsmai suna 'The Force Awakens' zai fito kasuwa a fadin duniya, to sai dai kuma ko ma'abota kallon fina-finai a India za su iya jira har sai wani makon domin su kalla.

Rahotanni sun ce masu kasuwancin fina-finai na jan kafa wajen fitar da fina-finai guda biyu wadanda ke gogayya da juna a Bollywood na kasar India.

Za a saki fina-finan ne a ranar Jumma'a. Fitar da fina-finai a rana guda tare da sabon fim din Star Wars, abu ne da masu kasuwancin fina-finai ke kaucewa ba wai a India ba kadai.

A India, za a saki manyan fina-finan Bollywood biyu watau fim din Bajirao Mastani da kuma Dilwale.

An dai jima ba a ga jarumi Shah Rukh Khan da Kajol a fim guda tare ba, sai a wannan karon cikin fim din Dilwale za a gansu tare, kuma a cikin shekarar nan an yi ittifakin cewa fim din Dilwale shi ne fim din da aka fi kashewa kudi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana kiran Shah Rukh Khan a matsayin Sarki Khan a India

Ana dai kallon Shahrukh Khan a matsayin jarumin da ya yi fice a Bollywood, fina-finansa ba wai a kasar India kawai suke tashe ba, har ma a kasashen waje, kuma fina-finansa a duk lokacin da ya yi su suna kasuwa a ko ina.

Ana sayar da tikitin shiga gidajen kallo da aka fi sani da Cinima a India da dama a duk lokacin da aka ce za a haska fim din Shahrukh Khan.

Yayin da aka fitar da fina-finai sama da dubu guda a cikin shekarar nan, fina-finan India su ne suka fi kasuwa.

To sai dai kuma duk da haka kudaden shigar da aka samu a fina-finan su ne mafi kankanta idan aka kwatanta da na sauran kasashe.

Bincike ya nuna cewa a cikin jerin sunayen jaruman da aka fito da su wadanda aka fi biya kudi idan sun yi fim, uku daga cikin su 'yan kasar India ne sai kuma Jackie Chan.

Yawanci an fi kallon fina-finai India a kasar ko kuma a makwabtanta, amma na Hollywood sun barbazu ko ina a duniya.

Image caption Fim din Dilwale shi ne fim na bakwai da Shah Rukh Khan da Kajol suka fito a tare

A cikin wata hira da ya yi kwanannan da BBC, Shahrukh Khan ya ce akwai bukatar masana'antar shirya fina-finai ta Bollywood ta canza tsarinta kana ta kuma fadada isar da fina-finanta zuwa kasashen waje inda magoya bayansu suke.

Shahrukh Khan ya ce "a cikin fim guda mai tsawon sa'oi biyu da rabi ayi wakoki biyar, gaskiya yakamata a canza wannan tsari."