'Shan giya da taba ne ke haifar da cancer'

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Sabon binciken ya karyata wani bincike da ke cewa ana kamuwa da cancer ne kawai sakamakon sakamakon sauyi a fasalin jerin kwayoyin halittar gado.

Wani sabon binciken kimiyya da aka yi a Amurka ya nuna cewa yawan shan taba da kwankwadar barasa ne ke sa mutane na kamuwa da kashi 90 cikin dari na cutar daji, wato cancer.

Masu bincike a Jami'ar Stony Brook da ke New York sun bayyana haka ne bayan sun sake yin nazari kan dalilan da ke haddasa kamuwa da cutar.

Sun gano cewa ba kasafai sauyi a fasalin jerin kwayoyin halittar gado shi kadan kan haifar da cutar daji ba, ba tare da gudunmawar wani abu daga waje ba, kamar gurbatacciyar iska da hasken rana mai cutarwa.

Binciken, wanda aka wallafa a mujallar kimiyya ta 'Nature', zai taimaka wajen sake yin nazarin yadda za a yi rigafakin kamuwa da cutar.

Wannan binciken dai ya karyata binciken da aka gudanar kafinsa, wanda ke ganin ana kamuwa da cancer ne kawai sakamakon sauyi a fasalin jerin kwayoyin halittar gado.