ECOWAS za ta haramta saka nikabi

Hakkin mallakar hoto
Image caption An haramta nikabi a Chadi da Kamaru

Shugabannin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS na kokarin haramta wa mata saka nikabi a yunkurin murkushe ayyukan mata 'yan kunar bakin wake.

Shugaban hukumar ECOWAS, Kadre Desire Ouedraogo ne ya bayyana haka a taron cika kungiyar shekaru 40 da kafuwa.

Ya ce dokar za ta "haramta irin siturun da ke hana jami'an tsaro gudanar da bincike".

A baya-bayan nan kungiyar Boko Haram na amfani da mata wajen kai hare-haren kunar bakin wake a Nigeria da Nijar da Chadi da kuma Kamaru.

Tuni kasashen Kamaru da Nijar da kuma Chadi suka haramta wa mata saka nikabi a matsayin riga-kafi daga hare-haren kunar bakin wake.