Batun 'yan gudun hijira zai mamaye taron EU

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tutocin tarayyar turai a taron kolin da ake yi a Brussels

Ana sa rai batun rikicin 'yan gudun hijira da ke shiga Turai zai mamaye tattaunawar taron kolin kungiyar kasashen Turai EU na shekara a Brussels.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da wasu shugabannin kungiyar kasashen Turan za su tattauna da Firayiministan Turkiyya domin lalubo hanyoyin sake tsugunar dubban 'yan gudun hijirar Syria dake Turkiyya.

Ana sa rai taron kolin zai tattauna hanyoyin kara tsaurara matakai a kan iyakokin kasashen Turan.

Taron zai kuma tattauna bukatar Burtaniya na inganta ka'idojin ci gaba da zama mamba a Tarayyar Turan, wanda Firayiminista David Cameron zai ba jama'a damar yin zaben raba gaddama a kai a 2017.