An rufe asusun FIFA kan cin hanci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amurka ce ta sa aka rufe asusun FIFA.

Hukumomi a Switzerland sun ce sun rufe asusu daban-daban na hukumar kula da kwallon kafar duniya, FIFA, inda hukumar ta ajiye miliyoyin dala.

Wani kakakin ma'aikatar shari'a ta kasar ya ce an dauki matakin ne bisa umarnin Amurka sakamakon binciken da take yi na karbar hanci a FIFA.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da kwamitin da'a na FIFA ke ganawa a kan daukaka karar da shugaban hukumar, Sepp Blatter, ya yi a kan dakatarwar da aka yi masa.

Mista Blatter da kansa zai bayyana a gaban kwamitin da ke yin bincike a birnin Zurich, duk da ikirarin da ya yi cewa akwai alamar tambaya kan yadda ake gudanar da binciken.

An dakatar da Mista Blatter har kwanaki 90 saboda ya bai wa shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Michel Platini $2m.

A ranar Juma'a ne za a saurari ba'asi daga wajen Mista Platini, ko da ya ke ya ce ba zai je gaban kwamitin ba saboda a cewarsa, an riga an yanke masa hukunci tun kafin a ji ta bakinsa.